Kotun koli ta Sanya ranar da za ta yanke hukunci kan Atiku da Obi a kan Tinubu

FB IMG 1697127697278 edit 3959534304081

Kotun kolin Nigeria ta sanya ranar Alhamis domin yanke hukunci kan karar da ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da na Labour, Peter Obi suka shigar.

Alfijir Labarai ta rawaito Mutanen biyu sun roki kotun kolin ne da ta yi watsi da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta yanke wanda ta tabbatar da zaben shugaban kasa Bola Tinubu.

Daraktan yada labarai na Kotun Koli, Dokta Festus Akande, a wata sanarwa a ranar Laraba ya ce an sanya ranar yanke hukunci kan kararrakin.

Kwamitin Gwamnatin Kano na tantance ma’aikatan da Ganduje ya dauka aiki ya mika rahotansa

Ya ce, “Gobe, Alhamis 26 ga watan October 2023, aka sanya domin yanke hukunci kan karar da Atiku da Peter Obi suka shigar suna ƙalubalantar nasarar Shugaban kasa Bola Tinubu.”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KpTjEvHUjd3CVzIQp8CSkZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *