Daga Nazifi Kwankwaso
Kotun sauraren korafin zabe dake nan kano tayi watsi da karar da Dan takarar majalisar jiha na jamiyyar APC a karamar hukumar bebeji Hon Auwal Ibrahim ya shigar gabanta Yana kalubalantar sahihancin Dan takarar majalisar jiha na jamiyyar NNPP hon Ali Mahd Tiga.
Alfijir Labarai ta rawaito Hon Auwal Ibrahim na jamiyyar APC yace Wanda yayi Kara ba Dan jamiyyar NNPP bane, Kuma yayin zabe an Sami aringizon kuri’u Wanda hakan ya sanya hukumar zabe ta inec ta bayyana shi a matsayin wanda yayi Nasara.

Da yake hukunci Mai sharia L B Owolaba yace Mai Kara ya gaza gabatar da kwararon hujoji da zasu gamsar da kotun, don haka kotun tayi watsi da karar nan take.
Lauyan jamiyyar NNPP Barista Bashir Yusif Muhd Tudun Wuzurchi yace, wajibi ne su godewa Allah bisa wanan Nasara, ya Kara da cewa zuwa yanzu jammiyarsu ta NNPP tayi Nasara a ƙararrakin zaɓe 13 da aka shigar dasu a kotunan sauraren korafin zabe.
Lauyan dake kare Hon Auwal ya aka tuntubebshi yaki cewa komai akan batun
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@musa_bestseller
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb