Hukumar yaƙi da fasa-ƙwaurin bil’adama ta Najeriya (NAPTIP), ta ce ta yi nasarar tabbatar da hukunci a kan wani masanin haɗa magunguna, Abubakar Danraka, wanda kotu ta yi wa ɗaurin rai-da-rai saboda laifin aikata fyaɗe.
Alfijir Labarai ta rawaito a sanarwar da hukumar ta wallafa a shafinta na sada zumunta ranar Talata ta ce, wata babbar kotun tarayya da ke unguwar Kubwa ce ta samu Abubakar Ɗanraka da laifi, kuma ta yanke masa hukuncin rai-da-rai a gidan gyaran hali.

A nasa bangaren Jami’in yaɗa labaran hukumar Mista Vincent Adekoye ya ce, Mai shari’a A. Akanbi-Yusuf ta yanke wa wanda aka yi ƙara hukuncin ne, bayan masu shigar da ƙara sun yi nasara tabbatar da hujjoji na yankan shakku.
A ranar 9 ga watan Agustan 2021 ne aka tuhumi mai laifin a gaban kotu,bayan tun farko ya musanta zargin da aka yi masa.
Sanarwar NAPTIP ta ce mai laifin, tsohon babban jami’in magunguna ne a Asibitin Ƙasa na Abuja, kuma an tuhume shi da laifin fyaɗe.
Ta ce a ranar 27 ga watan Maris ne aka kama mai laifin, bisa zargin lalata wata ƙaramar yarinya.
Hukumar ta zargi Abubakar Ɗanraka da yaudarar yarinyar zuwa ɗakinsa, inda ya neme ta, ta dubura bayan ya gauraya ƙwaya cikin abin shan da ya ba ta.
Hukuncin, ya kawo ƙarshen shari’a mai cike da taƙaddama, da aka shafe tsawon shekara uku ana tafkawa.
Sanarwar dai ta kuma ambato babbar daraktar hukumar NAPTIP, Farfesa Fatma Waziri-Azi, tana yaba wa hukuncin, wadda ta ce zai kasance izina ga masu yunƙurin aikata irin wannan laifi.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb