Kotu ta tsare wasu mutane 4 da suke buga Ludo da shan kwayoyi a cikin Masallaci a Kano

Screenshot 20221014 081451 com.android.chrome edit 14830240241485

Wata Kotun Shari’ah ta Kano da ke zamanta a Gama PRP ta bayar da umarnin tsare wasu mutane hudu da ake zargi da yin ludo da shan kayan haram a cikin masallaci.

Alfijir labarai ta rawaito Wadanda ake zargin sun hada da Sadik Ibrahim, Jamilu Ibrahim, Umar Ibrahim, da Adamu Ibrahim duk mazauna unguwar Rimin Kebe ne.

Tun da farko wani Auwalu Usman da ke wannan unguwar ya yi korafin cewa mutanen hudu sun hada baki suka shiga masallaci domin yin wasan ludo da shan haramtattun abubuwa.

Ya ce yayin da ya yi yunkurin hana su, sai suka taru suka yi masa dukan tsiya tare da yi masa gargadin yin katsalandan a harkokinsu.

Wanda ake kara na farko ya amince da laifin da ake tuhumarsa da shi yayin da sauran ukun suka musanta zargin da ake yi musu a lokacin da mai gabatar da kara, Aliyu Abidin Murtala ya karanta musu tuhume-tuhumen.

Alkalin kotun, Malam Nura Yusuf Ahmed, ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare su a gidan gyaran hali har zuwa ranar 3 ga watan Janairun 2024, domin gabatar da shaidu a gaban kotu.

Daily Trust

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *