Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen yan majalisun tarayya karkashin jagoranci mai shari’a Flora Ngozi Azine, ta tabbatar da Hon Sani Adamu Wakili na jam’iyyar NNPP, a matsayin halattaccen dan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Minjibir da Ungogo.

Alfijir Labarai ta rawaito hukuncin kotun da tayi a wannan ranar kotun ta ci tarar mai shigar karar tsohon majalisar tarayyar mai wakiltar kananan hukumomin Minjibir da Ungogo na jam’iyyar APC, Hon Sani Ma’aruf Mai Wake naira 600,000 sakamakon bata lokacin hukumar zabe mai zaman kan ta da Sani Adamu Wakili da Kuma jam’iyyar NNPP a gaban kotun.
Hon Sani Ma’aruf Mai Wake ya shigar da karar ne domin kalubantar nasarar Hon Sani Adamu Wakili na jam’iyyar NNPP wanda hukumar zabe mai zaman kan ta tabbatar dashi bayan kammala babban zaban kasar nan.
Barista Abdulkarim Kabir Maude Minjibir shine lauyan Sani Adamu Wakili ya bayyana cewa bangaran masu karar sun zagin jam’iyyar NNPP da yin arangizon kuru’u da dakuma hada wasu kada kuri’ar tasu a lokacin gudanar da babban zaban kasar nan.
Minjibir ya Kara da cewa hujujjin da bangaran masu karar suka kasa kawo wa gaban kotun a dan hakan ne ma mai shari’a Flora Ngozi tayi watsi da bukatar masu karar tare da tabbatar da nasarar Sani Adamu Wakili.
Sai dai Kuma tawagar lauyoyin Sani Ma’aruf Mai Wake sun bayyana wa manema labarai cewa zasu yi nasarar hukuncin kotun kafin daukar mataki na gaba.
mu info@oddity24.com.ng ko a nambar waya 07018545131 kazalika wanna shafi na www.oddity24.com.ng sai ya yi tankade da rairaya akan dukkanin wani labari da zai wallafa domin samun daidaito a tsakanin al’umma.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@musa_bestseller
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb