Alfijr ta rawaito Babbar Kotun Tarayya a jihar Kano ta yanke hukuncin cewa Muhammad Abacha ne ɗan takarar gwamnan jihar a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.
Mai Shari’a A M Liman ne ya yanke hukuncin a ranar Alhamis ta manhajar Zoom kasancewar baya gari.
Ya ce bangaren da suka gudanar da zaben fitar da gwani a Lugard Road shi ne halastaccen zaben dan takarar gwamnan na jam’iyyar PDP.
Tun bayan ficewar Rabi’u Musa Kwankwaso ne rikici ya ƙara ƙamari a jam’iyyar PDP ta Kano ta yadda har aka samu rarrabuwar kawuna a zaɓen fitar da gwani na ɗan takarar gwamna.
Ɓangaren Aminu Wali ya fitar da ɗan takararsa Sadiq Wali yayin da ɓangaren Shehu Sagagi ya fitar da Muhammad Abacha a matsayin nasa ɗan takarar.
A zaben fitar da gwani da aka yi a watan Mayun 2022 Mohammed Abacha ya fafata da Adamu Yunusa Ɗan Gwani da Ibrahim Al-Amin Little da Muhiyi Magaji Rimin Gado da Jafar Sani Bello da kuma Injiniya Mu’azu Magaji wato Ɗan Sarauniya.
Kuma a lokacin sakamakon ya nuna Muhammad din ne ya yi nasara.
Sai dai a watan Yuli kuma sai ga hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta wallafa sunan Sadiq Aminu-Wali a matsayin dan takarar PDP na jihar Kano.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇