Kotu Ta Kori Karar Da Ake Kalubalantar Muhammad Abacha,

Alfijr ta rawaito wata babbar kotun tarayya a jihar ta kori karar da ke kalubalantar tsayar da Mohammad Abacha, a matsayin dan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar PDP a zaben 11 ga Maris, 2023.

Kotun ta yi watsi da karar da wanda ya kalubalantar sa, Jafar Sani Bello ya shigar, yana mai rokon kotun ta soke sunan Abacha.

Ballo, dan takarar gwamna, wanda ya zo na biyu a bayan Abacha a zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP a Kano, a cikin karar mai lamba: FHC/KN/CS/186/2022 ya nemi a soke zaben Abacha.

Mai shigar da karar wanda ya nemi ya maye gurbin Abacha a matsayin dan takarar jam’iyyar, ya yi ikirarin da sauran cewa, sunan Abacha ba ya cikin rajistar zama mambobin jam’iyyar PDP a Ward Fagge, karamar hukumar Fagge ta Jihar Kano, don haka bai cancanci tsayawa takara ba. In Ji Jafar

A wani hukunci da mai shari’a A. M. Liman ya yanke, cewa rashin sunan Abacha a rajistar jam’iyyar PDP a Fagge bai isa ya hana shi tsayawa takara ba.

Mai shari’a Liman, wanda ya tabbatar da hujjojin da lauyan Abacha, Reuben Atabo (SAN) ya yi, ya kuma ce katin zama dan jam’iyyar PDP da aka ba Abacha da kuma soke zaben da jam’iyyar ta yi masa ya isa ya kai shi zaben fidda gwani.

Leadership

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *