Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta fitar da sanarwar gargadi ga kwamishinan aiyuka na jihar Marwan Ahmad kano bisa kokarin sa na bijirewa umarnin da ta yi wa gwamnatin jihar.
Alfijir Labarai ta rawaito a baya dai kotun ta bayar da umarnin a ranar 29 ga watan Satumba, inda ta haramtawa gwamnatin jihar Kano shiga ko yin wani aiki a filin Idi na Kano, dake Kofar Mata a cikin birnin Kano.
Lauyan da ke wakiltar Kungiyar masu shaguna a filin Idi , Dr Nuraddeen Ayagi, ne ya garzaya kotu inda ya bukaci a yi wa Kwamishinan gargadi game da illar kin bin umarnin kotu.
An shaida wa kotun cewa Kwamishinan ya ci gaba da shiga tare da lalata dukiyar da ke filin idin, duk da hukuncin kotun.
Dokta Ayagi ya ce yin watsi da umarnin kotu yana zubar da kima da mutuncin sha’ari, kuma bai kamata a dauki irin wadannan ayyuka da wasa ba.
Ya ci gaba da cewa kotun tana sa ran gwamnatin Kano ta bi umarninta sau da kafa, kuma rashin yin biyayya ga umarnin zai iya sawa kotun ta dau matakin da ya dace akan wanda ya sabawa umarnin ta.
Kotun ta tunatar da Marwan Ahmed cewa rashin bin umarnin kotun na iya kai wa a yiwa mutum hukuncin raina kotu wanda kuma zai iya kaiwa ga dauri.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo