Kotu Ta Daure Ƴar Tsohon shugaban kasa Shekaru Biyar A Gidan Gyaran Hali

Alfijr ta rawaito Faezeh Hashemi, ƴar Akbar Hashemi Rafsanjani, tsohon shugaban kasar Iran, mai shari’a ya aike da ita gidan gyaran hali da Tarbiyya na shekaru biyar.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da Lauyanta ya tabbatar a ranar Talata.

Hukuncin da aka yanke mata ne biyo bayan zargin da ake yi mata na tada tarzoma a ƙasar.

Wata majiya ta bayyana cewa mai gabatar da kara na Tehran ya tuhumi Hashemi da laifin ” farfaganda ga tsarin mulkin ƙasar” a bara.

An tsare ta a Tehran a lokacin zanga-zangar bayan da wata matashiyar Kurdawa ta mutu yayin da take hannun ‘yan sanda, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka ruwaito daga watan Satumba.

Majiyar ta tabbatar da kama ta ne saboda tada tarzoma.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *