Kotu ta daure wasu yan Tiktok 4 a Kano biyo bayan rashin mutunci da suke yi a Kano

IMG 20240111 234351

Kotu  a Kano ta aike da wasu matasa hudu ‘yan TikTok gidan gyaran hali bisa zargin yada rashin tarbiyya a kafafen sada zumunta biyo bayan kararsu da Hukumar tace fina finai tayi

Wadanda ake tuhuma su ne Hafsa Hamisu (Zoom Zoom), Usman Majidadiɓ (Majidadi), Sumayya Muhammad (Summy Beby), da Usman Ibrahim (Maikalar Kudi), kuma duk sun amsa laifin da ake tuhumarsu da shi.

Hukumar tace fina finai ta jihar Kano karkashin jagorancin Abba El- Mustapha ta sha alwashin ci gaba da yaki da rashin da’a a kafafen sada zumunta domin kare tarbiyya da al’adun al’umma bisa koyarwar addinin Musulunci.

Freedom Radio

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *