Wata babbar kotun jiha da ke zamanta a Miller Road Kano ta dakatar da gwamnantin Kano daga yin rusau a gine-ginen da ke jikin Badala akan titin zuwa jami’ar Bayero.
Alfijir Labarai ta rawaito Wannan na zuwa ne bayan da mamallaka wuraren suka roki kotun da ta duba halin da suke ciki, la’akari da cewar bu sa karya ka’ida ba wajen mallakar wuraren.
Mai shari’a Hafsat Yahya Sani ce ta bayar da umarnin dakatarwar har sai kotu ta kammala nazari akan al’amarin.
Haka kuma ta sanya ranar alhamis 26 ga Oktoba mai zuwa a matsayin ranar da za a saurari shari’ar.
A baya dai gwamnatin jihar kano karkashin jagorancin Gwamna Engr Abba Kabir Yusuf ta sanyawa gine-ginen jikin badala jan fenti wanda hakan ke nuna cewa kowanne lokaci za’a iya rushe gine-ginen, saboda abun da gwamnatin ta kirawo da cewa an yi gine-ginen ne ba bisa ƙa’ida ba.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb