Wata babbar kotu da ke zamanta a jihar Legas ta bayar da belin Godwin Emefiele, dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya CBN a kan kudi naira miliyan 20.
Alfijir Labarai ta rawaito a wani hukunci da ya yanke a safiyar Talata, Nicholas Oweibo, Alkalin kotun, ya ce tuhumar da ake yi wa Emefiele na da beli.
An bayar da Belin ne da sharadin kudi da mutum daya wanda zai tsaya masa.
A baya kotun ta yi watsi da ikirarin da gwamnati ta yi na cewa ba ta samu kwafin takardar belin da Emefiele ya shigar ba a shari’ar da ake yi masa na mallakar bindiga.
Mai shari’a Oweibo ya ce akwai shaidun da ke nuna cewa ana iya bada Belin nasa.
Lauyoyin Emefiele ne karkashin jagorancin Joseph Dauda, SAN suka shigar da bukatar belin.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb