Kotu Ta Ɗaure Wani Direba Mai Shekaru 56 Ɗaurin Rai Da Rai

Wata kotu da ke zamanta a Ikeja ta yankewa wani direban mota mai suna Folarin Rauf hukuncin daurin rai da rai a kan laifin yi wa jikarsa mai shekaru biyar fyade a Legas.

A ranar Litinin ne alkalin kotun, Abiola Soladoye, ya samu Rauf da laifin lalata da yarinyar.

A watan Nuwamba 2021, aka gurfanar da direban a gaban kuliya bisa tuhumar lalata da yarinya, kuma ya musanta aikata laifin.

A yayin shari’ar, tawagar masu gabatar da kara ta kira yarinyar da wasu shaidu uku domin su ba da shaida a gaban kotun.

Rundunar Yan sanda ta gabatar da wanda ake kara ne kawai a matsayin shaida.

Da ake tambayarta a gaban kotu, ta shaida wa mai shari’a cewa Rauf ya yi mata fyade a lokuta da dama a cikin dakin kakan da kuma cikin wata mota kirar Jeep.

A nasa bangaren mai shari’a yayin yanke hukuncin ya ce masu gabatar da kara sun tabbatar da cewa wanda ake tuhuma ya yi wa yarinyar fyade, wadda ‘yar karama ce.

Alkalin ya bayyana abin da wanda ake tuhumar ya aikata a matsayin “mummunan hali ne da rashin imani”, ta kara da cewa dole ya biya diyya kan wannan katobarar.

Masu kare wanda ake kara a cikin rubutaccen jawabinsu sun bukaci kotu da ta sallami wanda ake kara saboda babu wata shaida kwakkwara a kansa.

Sai lauyoyin jikar tasa sun bayyana cewar, wanda ake tuhuma yana da mummunan hali, ba shi da imani, ga rashin hankali, wanda hakan nr ya kai shi ga lalata jikarsa.”

DSVA REACTS Da take mayar da martani ga hukuncin, Hukumar Yaki da Cin Hanci da Jama’a ta Jihar Legas (DSVA), a cikin wata sanarwa a ranar Talata, ta ce za a saka sunan wanda aka yankewa hukuncin cikin jerin sunayen masu laifin lalata a jihar.

Hukumar ta ce an yi adalci kan laifin da wanda aka yanke wa hukuncin da ya aikata.

“Hukuncin da mai shari’a Abiola Soladoye ya zartar yana nuna gagarumar nasara a yaki da laifukan fyade da cin zarafi a cikin gida, kuma ya zama gargadi ga masu aikata laifuka cewa za a yi adalci a koyaushe,” in ji hukumar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *