Kasar Saudiyya Ta Sanar Da Ganin watan Babbar Sallah

Alfijr
Alfijr ta rawaito Kasar Saudiyya ta sanar da ganin watan Dhul Hijjah na Babbar Sallah, sanarwar ta ce gobe Alhamis 30 ga watan Yuni ne daya ga wata.

Sanarwar ta fita ne ta Shafin da ke kula da masallatai biyu masu daraja na Haramain Sharifain a Facebook da Twitter

Alfijr

Ranar Juma a 8 ga watan Yuli ita ce za a gabatar da tsayuwar Arfat

Babbar sallar a nan Nijeriya za ta kama ranar Asabar 9 ga watan Yulin 2022 da yardar Allah.