Kasafin kudin 2024: Yadda Majalisar Wakilai ta ware N6.6trn ga ayyukan da ba a san su ba’ a ma’aikatu 20

FB IMG 1710198919187

Daga Aminu Bala Madobi

Ma’aikatun da aka zaba sun hada da Maaikatar Matasa, Wasanni, Tsaro, Harkokin Waje, Ayyuka na Musamman, Kasafin Kudi da Tsare Tsaren Tattalin Arziki, Yawon shakatawa, Shari’a da ta albarkatun Man Fetur.

Alfijir labarai ta rawaito cikin makonnin da suka gabata labarin cushe kasafin kudin bana da majalisar wakilai ta 10 ya karade ko ina.

A cikin zargin da Sanata Abdul Ningi Mai Wakiltar Bauchi ta tsakiya yayi wanda ta kaiga an dakatar da shi na tsawon watanni 6, Jaridar Economic Confidential ta tattaro cewa majalisar wakilan karkashin Sanata Godswill Akpabio ta amince da kudi sama da Tiriliyan8tr N8,447,887,443,379 domin gudanar da manyan ayyuka a ma’aikatun gwamnatin tarayya guda 20 a cikin dokar kasafi ta bana.

Ma’aikatun da aka zaba sun hada da Maaikatar Matasa, Wasanni, Tsaro, Harkokin Waje, Ayyuka na Musamman, Kasafin Kudi da Tsare Tsaren Tattalin Arziki, Yawon shakatawa, Shari’a da ta albarkatun Man Fetur.

Sauran su ne Maaikatar Al’adu, Harkokin Mata, Ilimi, Harkokin ‘yan sanda, Sadarwa da Tattalin Arzikin zamani, Noma, Albarkatun Ruwa, Muhalli, Lafiya, Ma’adanai da Ayyuka.

Sai dai abin mamaki shine an ware sama da tiriliyan 6 wato N6,671,810,092,564 (a cikin N8,447,887,443,379), wanda ke wakiltar kusan kashi 71.98 na jimillar kasafin ayyuka na musamman da ba asan inda suke ba.

A halin da ake ciki, wasu ayyukan da ke da takamaiman wurare ba su cikin ka’idojin doka na ma’aikatu ko hukumomi kuma galibi suna aiki ne da ƙungiyoyi.

Da take nazarin takardar, Economic Confidential ta lura cewa kimanin samada tiriliyan 2tr N2,486,098,619,722 (a cikin jimillar kasafin N8,447,887,443,379 an ware su ne don gudanar da manyan ayyuka na ma’aikatun 20 da aka zabo.

Hakazalika, an ware ƙarin N4,185,711,477,842 don ayyukan da ba su da takamaiman gurare ko yankin da za agudanar da ayyukan ba, wanda hakan ke dagula hanyoyin ganowa da tantance su.

Dangane da abin da shiyyoyi 6 suka samu (na manyan ayyuka) a ma’aikatu 20, Economic Confidential ta gano cewa an ware wa yankin Kudu maso Yamma samada Bilyan 419 wato N419,917,163,300 yayin da Kudu maso Gabas ya samu N537,086,249,684. Sauran sun hada da Kudu-maso-Kudu (N224,969,978,366), Arewa maso Yamma (N365,387,892,588), Arewa maso Gabas (N349,434,063,602) da Arewa ta tsakiya (N730,029,622,125).

A Ma’aikatar Matasa ta Tarayya an ware Naira miliyan 5,096,411,496 don gudanar da ayyuka daban-daban a fadin shiyyoyin siyasar kasa guda shida. Abin takaici, ba a nuna yankin da ayyukan da suka kai N2,868,851,764 ba (a cikin N5,096,411,496).

A ma’aikatar wasanni ta tarayya, an ware naira 21,614,361,733 domin gudanar da ayyuka daban-daban a shiyyoyin siyasa guda shida. Abin bakin ciki, ba a bayyana yankin da ayyukan da ya kai N7,464,061,733 (a cikin N21,614,361,733) ba.

Hakazalika, a ma’aikatar tsaro ta tarayya, an ware Naira miliyan 3,762,721,808,585 don gudanar da ayyuka daban-daban na manyan ayyuka a shiyyoyin siyasar kasa shida. Duk da haka, ba a ambaci yankin da ayyukan da ya kai N3,280,130,880,602 (a cikin N3,762,721,808,585).

Bugu da kari, Ma’aikatar Kasafin Kudi da Tsare Tattalin Arziki ta Tarayya ta ware Naira 2,293,112,174,749 don gudanar da manyan ayyuka daban-daban a shiyyoyi shida na siyasa. Abin takaici, ba a bayyana yankin da ayyukan da suka kai N383,729,998,776 (cikin N2,293,112,174,749).

Hakazalika, akan Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur ta Tarayya, an ware Naira miliyan 8,622,741,732 don gudanar da ayyuka daban-daban na manyan ayyuka a shiyyoyin siyasar kasa shida. Duk da haka, ba a ambaci yankin da ayyukan da ya kai N8,554,622,753 (a cikin N8,622,741,732).

A ma’aikatar shari’a ta tarayya, an ware naira biliyan 33,860,593,566 domin gudanar da ayyuka daban-daban a shiyyoyin siyasar kasa guda shida. Wani abin mamaki shi ne yankin da ayyukan da ya kai Naira miliyan 25,742,716,841 (a cikin Naira 33,860,593,566) na bukatar a tantance.

Ma’aikatan ‘yan sanda ta tarayya, an kashe jimillar Naira miliyan 99,382,436,919 domin gudanar da ayyuka daban-daban a shiyyoyin siyasar kasa guda shida, kamar yadda takardar ta bayyana. Duk da haka, ba a ambaci yankin da ayyukan da suka kai N49,090,806,535 (cikin N99,382,436,919) ba.

Haka kuma, akan Ma’aikatar Aikin Gona ta Tarayya, an ware N895,398,209,400 don gudanar da manyan ayyuka daban-daban a shiyyoyin siyasa shida. Abin takaici, ba a nuna yankin da ayyukan da ya kai N124,131,394,058 (a cikin N895,398,209,400).

A ma’aikatar sadarwa da tattalin arziki na zamani ta tarayya, an ware Naira miliyan 4,893,877,166 domin gudanar da ayyuka daban-daban a shiyyoyin siyasar kasa guda shida. Amma yankin da ayyukan da suka kai Naira 3,646,711,848 (cikin N4,893,877,166) ba a ambata ba.

A ma’aikatar lafiya ta tarayya kuma, an ware naira biliyan 539,413,163,575 domin gudanar da ayyuka daban-daban a shiyyoyin siyasar kasa guda shida. Abin bakin ciki, yankin da ayyukan da ya kai N146,215,196,278 (a cikin N539,413,163,575) ba a bayyana ba.

A ma’aikatar ayyuka ta tarayya, an ware naira biliyan 987,289,797,899 domin gudanar da ayyuka daban-daban a fadin shiyyoyin siyasar kasa guda shida. Abin takaici, ba a bayyana yankin da ayyukan da suka kai N44,428,040,905 (cikin N987,289,797,899).

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *