KAROTA Ta Shirya Tsaf Don Fara Kaman Masu Adaidaita Sahu

 KAROTA Ta Shirya Tsaf Don Fara Kaman Masu Adaidaita Sahu

Best Seller Channel 

 Best Seller Channel 

Best seller channel ta rawaito, hukumar karota tace zata fara damke masu tuka adaidaita sahu da suka yi burus da sabunta takardun su na  tukinsu. 

Shugaban Hukumar Baffa Babba Dan-Agundi, ne ya bayyana hakan a Kano lokacin da yake zantawa da manema labarai kan tsare na aikin Sabuwar Shekara da hukumar zata tunkara a 2022. 

Ya tabbatar da matakin zai zama gargadi ga mahaya da suka kasa sabunta takardar su. 

Best Seller Channel 

Baffa ya Kara da cewa, wadanda suka kasance wannan shine karon su na farko wajen yin takardun za su biya naira 18,000, yayin da wadanda suke da shi za su biya naira 8,000. 

Baffa ya kuma ce hukumar ta hada da hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) reshen jihar domin kama masu kunnen Kashi, don mika su ga hukumar domin daukar matakin da ya dace.  

Best Seller Channel 

A cikin sabbin tsare-tsarenmu na 2022, KAROTA zasu fara damke duk Wanda  da ba su da mitar da ke kayade gudun ababen hawa don ladaftar dasu suma inji Baffa. 

Ya kuma ce hukumar ta dauki sabbin ma’aikata 1,000 a aikin 2021 tare da kara motocin aiki daga uku zuwa 60, da kuma sabbin mashina tsere guda 50 don samun ingantattun kayan ayyukan Hukumar.