Karin Albashi! Ma’aikatan Nijeriya Za Su Dara A 2024 – in Ji Shugaba Tinubu

FB IMG 1704100007026

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce za a yi wa ma’aikatan Nijeriya ƙarin albashi a wannan shekarar ta 2024.

Alfijir labarai ta rawaito Shugaban ya kara da cewa “za mu kara albashin kowanne ma’aikaci a Nijeriya, domin ƙarin shi ne abu mafi dacewa”

Dole Ne Mu Tabbatar Da Zaman Lafiya da kwanciyar hankali a Nijeriya. Da yake jawabin sabuwar shekara a jihar Legas shugaba Tinubu, ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da an samar da ababen more rayuwa da kuma inganta tattalin arzikin ƙasar da zai kawo saukaka rayuwar ma’aikata da ‘yan Nijeriya.

“Gwamnatinmu za ta yi aiki tuƙuru domin tabbatar da mun taɓa rayuwar kowanne dan Nijeriya” inji shi.

Tinubu ya ce “Zuwa yanzu muna dab da kammala shirye-shiryen da muka kwashe watanni 7 da suka gabata na farfaɗo da tattalin arziki, domin samar da ababen more rayuwa ga ‘yan Nijeriya baki daya.

Shugaba Tinubu ya kuma yi tsokaci kan irin kokarin da gwamnatinsa ke yi wajen ganin an inganta bangaren samar da wutar lantarki, duba cewa ba za a iya samun ci gaban da ake da bukata ba, ba tare da wutar lantarki ba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

One Reply to “Karin Albashi! Ma’aikatan Nijeriya Za Su Dara A 2024 – in Ji Shugaba Tinubu”

  1. Yakamata al’ummar Nijeriya, musamman ‘yan midiya su kara kaimin shaiadawa Shugaba Tinibu ya soke bashin da Buhari ya dorawa ‘yan Nijeriya na kudin KORONA ya maida shi tallafi, saboda irin kuncin rayrayuwa da suke ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *