Karancin Naira: Gwamna Ya Umurci Jami’an Tsaro Da Su Kamo Wasu Masu PoS

Alfijr ta rawaito Gwamnan jihar Ebonyi David Umahi ya umurci jami’an tsaro da su kama tare da gurfanar da ma’aikatan POS da ke karbar makudan kudade a jihar.

Umahi ya gargadi masu gudanar da POS a jihar da su daina karbar Kuɗaɗen da ya wuce kima daga hannun mutane ko kuma su kasance a shirye su tunkari hukumomin tsaro da gwamnatin jihar Ebonyi.

Ya koka da cewa kudin da ma’aikatan POS ke karba ya wuce gona da iri, ya kara wa ‘yan Najeriya radadin da a halin yanzu suke ciki kan manufar musanya Naira.

Ya yi wannan jawabi ne a yayin wani watsa shirye-shirye ga al’ummar jihar kan al’amuran zaman lafiya da tsaro a jihar, ranar Juma’a.

Na kuma umurci jami’an tsaro da su kama su gurfanar da duk wanda ya karya mana dokar

Dangane da yadda aka dakile zanga-zangar da kuma yunkurin kawo tashin hankali na kawo cikas ga zaman lafiya a jihar Ebonyi, musamman a harabar babban bankin kasa da sauran bankunan kasuwanci da wasu fusatattun mazauna jihar suka yi, ya godewa jami’an tsaro da suka yi riga-kafin lamarin.

Da yake magana kan rikicin da ya dabaibaye manufar musanya naira, Umahi ya ce yana da yakinin cewa ko shakka babu shugaban kasa Muhammadu Buhari da kotun koli da kuma gwamnonin jihohi za su yi sulhu cikin lumana don warware matsalolin da ke tasowa daga manufar musanya naira.

Umahi ya ce: “Ina da yakinin cewa wahalar da ake fama da ita a yanzu ba za ta ci gaba ba, kasancewar shugaban kasa da kotun koli za su yi sulhu cikin lumana, kuma hakika gwamnonin za su warware wadannan matsalolin ta yadda jama’armu za su sake yin murmushi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *