Kamfanin BUA Ya Ƙara Farashin Sikari, Fulawa, Da Spaghetti Bayan Ya Rage Farashin Siminti

FB IMG 1696915532733

A wani yunkuri na ban mamaki, kamfanin BUA Ya Ƙara Farashin sikari, fulawa, da spaghetti, bayan sanar da Rage Farashin siminti.

Alfijir Labarai ta rawaito bayan wani bincike da ta Gudanar a Kasuwar Kano ya nuna cewa kamfanin na BUA Ya kara farashin sikari da fulawa da kuma taliya A shahararriyar Kasuwar Singa ta Kano, Yanzu haka ana siyar da sukari kan Naira 47,500 kan Kowanne buhu wani wajen ma yafi haka, Spaghetti kan katan Naira 9,000, da buhun fulawa a kan Naira 34,500.

Wani dillalin kayayyakin na BUA a Kano ya ce ƙarin Farashin ya biyo Bayan da kamfanin ya sanar da rage farashin siminti. “Mun lura da ƙaruwa a cikin makon nan, Farashin buhun Gari yanzu ya haura N34,500 saɓanin Naira 31,000 Zuwa N32,000 da aka sayar a makon da ya Gabata, an kara Kusan Naira 2,000 a buhun fulawa A farashin kamfani.” inji dillalin.

“Akan sikari Babu wani farashi mai inganci amma ana sayar dashi har zuwa N48,000 zuwa sama.

A satin da ya Gabata ana siyar da shi akan kuɗi naira 44,500 Zuwa Naira 45,000, Wani yace min yana siyar dashi akan N46,500.

Dillalin ya ce “An sanar da mu game da ƙarin kudin da aka yi a wannan makon, yawanci suna tattaunawa damu ta hanyar wayar tarho.

Ina kuma so in gaya muku cewa duk waɗannan farashin, daga kamfani ne,” inji dillalin.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *