Daga Aminu Babba
Dubun wasu ɓarayi ta cika ne a unguwar Ladanai layin Tsamiya Ring road dake birnin Kano
Alfijir Labarai ta rawaito ɓarayin sun dirfaffi wata katuwar mota ne da aka ajiye da tarin kayan masarufi, sun zo ne da wata karamar motar su.
Wani ganau ya shaidawa wakilin Alfijir Labarai cewar Barayin sun yanka tambol din motar ne bayan sun ɓoye motarsu a baya.
Bayan da suka yi ta waige waige basu ga kowa ba, sai suka fara diban kayan suna zubawa a motar su.
Ni kuma dake a kusa da wajen nake aikina ga kuma cikin dare ne kusan asuba, sai naji tsoron kai na tunkare su, koda makami a wajensu, kuma bani da lambar wanda zan kira. In ji ganau din.
Sun debo kaya suna zubar da wasu da sun ga hasken fitila sai su labe, sai motar ta wuce sai su ci gaba.
Bayan gama kwasar kayan sai sun shiga motarsu sun yi kokarin tashinta domin su gudu, sai ta ki tashi, sun yi kokarin tura motar domin ta tashi amma ina! Sai ga jami an tsaro nan sun zo wajen da motarsu, nan da nan suka sha kansu, ɓarayin suka fita daga motar suka ranta a na kare.
Bayan naga mutane sun fara fitowa, sai nazo wajen motar na tsaya, nace bara muje mu gayawa mai mota tunda shi bai san me yake faruwa ba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo