Alfijr ta rawaito Kamfanin Jiragen Sama na Saudiyya ya sanar da shirinsa na komawa jigaila a filin jirgin saman malam Aminu Kano da ke birnin Dabo daga ranar Talata, 3 ga Janairu, 2023.
Hakan na kunshe ne cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 29 ga watan Disamba ta aikewa da ALL TRAVEL AGENCY AND NANTA, inda ta ce za a fara gudanar da jigilar ne da ranaku uku na mako ( Talata, Alhamis da Asabar) tare da tashi daga Jeddah da karfe 12:50 na rana sannan kuma ya sauka a Kano da karfe 15:40 na yamma.
Zai kuma sake tashi daga karfe 18:15 suka tashi Kano suka isa Jidda da karfe 00:40.
Wasikar ta kuma bayyana cewa masu dauke da bizar Umrah su kai rahoto da fasfo na zahiri, tikiti da biza don tantancewa da amince wa.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
Ma shaa Allah.
Ma shaa Allah