Jihohi 6 Sun Gurfanar Da INEC Gaban Kotun Koli Kan Zaɓen Shugaban Ƙasa

Alfijr ta rawaito Jihohi shida na tarayyar Najeriya sun maka gwamnatin tarayya a gaban kotun koli, kan halin da ake ciki, tattarawa da kuma sanar da ranar 25 ga watan Fabrairu 2023, Kan zaben shugaban kasa da na majalisar dokoki ta kasa.

Jihohin da suka hada da Adamawa, Akwa-Ibom, Bayelsa, Delta, Edo da Sokoto, suna son kotun koli ta bayyana cewa Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da hukumar zaben kasar ta sanar da aka gudanar bai yi nasara ba.

Sun yi nuni da cewa gaba daya sakamakon zaben shugaban kasa da shugaban hukumar zabe ta INEC ya sanar a cibiyar tattara bayanai ta kasa da ke Abuja, ya sabawa tanadin dokar zabe.

A cewarsu, suna son a bayyana cewa rashin saka sakamakon kowane rumfunan zabe 176,974 a fadin kasar, dangane da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin kasar, bai dace da tanadin dokar zabe ba.

hdrpl

Ku tuna cewa INEC ta bayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa a ranar Laraba.

Hukumar zaben ta kuma ba Tinubu takardar shaidar cin zabe.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *