Jarumin Fina-Finan Nollywood Mista Ibu Ya Rasu Bayan Fama Da Rashin Lafiya

FB IMG 1709420962753

Fitaccen jarumin masana’antar Nollywood, John Okafor wanda aka fi sani da Mista Ibu ya riga mu gidan gaskiya.

Mista Ibu wanda ya shahara a matsayin jarumin barkwanci ya mutu yana da shekara 62.

Mista Ibu ya mutu ne a asibitin Evercare da ke Lekki a birnin Ikkon Legas.

Tuni dai magoya baya musamman a dandalan sada zumunta suka shiga alhini, inda suke tunatar da juna irin fina-finan da marigayin ya haska.

A watan Nuwambar bara ne aka yi wa Mista Ibu tiyatar guntule ɗaya daga cikin kafafunsa sanadiyyar ciwon suga da ya addabe shi.

A watan Satumbar bara ne wani bidiyo da Mista Ibu ya wallafa a shafinsa na Instagram ya karaɗe shafukan sada zumunta, inda aka naɗo shi yana neman taimako da kuma addu’a wajen magoya bayansa.

Labarin rasuwarsa na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 da rasuwar Quadri Oyebamiji wanda aka fi sani da Sisi Quadri, wani tsohon jarumin Nollywood

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

One Reply to “Jarumin Fina-Finan Nollywood Mista Ibu Ya Rasu Bayan Fama Da Rashin Lafiya”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *