Alfijr ta rawaito jarumar masanaantar Kannywood Amal Umar, ta roki wata babbar kotun tarayya da ke Kano inda ta bukaci da ta dakatar da kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano CP da tsare ta bisa zargin almundahanar kudi naira miliyan 40.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano a shekarar da ta gabata ta fara gudanar da bincike a kan jarumar kan zargin hada baki da watan Ramadan, wanda ake zargin saurayinta ne, domin damfari wani dan kasuwa, Alhaji Yusuf Adamu. Dan kasuwar ya zarge ta da karbar kudinsa da yarjejeniyar cewa za su kafa sana’ar wayar salula.
Sai dai jarumar ta garzaya kotu, karkashin jagorancin Sunusi Ado Magaji, wanda ya dage ci gaba da sauraron karar zuwa wannan watan.

A lokacin da kotun ta ci gaba da zama a ranar Juma’a, lauyan gwamnatin jihar, Barr Badamasi, ya gabatar da wasu takardu da suka nuna yadda jarumar ta damfari mutumin kudi N40m.
Sai dai Amal Umar ta bakin lauyanta Barr. Adama Usman, ta ce mai shigar da karar ya ba ta N8m ne kawai don ta bude shago, sannan ya ba ta N3m domin ta biyawa mahaifinta bashi.
Ta kuma gabatar da takardun da ke kare furucinta.

Don haka Barr Adama, ya bukaci kotun da ta haramtawa ‘yan sanda gudanar da bincike da kuma yunkurin cafke wanda yake karewa.
Mai shari’a Magaji ya dage sauraron karar zuwa ranar 17 ga Afrilu, 2023.
Daily Trust

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇