
Alfijr ta rawaito Kimanin iyayen marayu Sama da 200 ne suka Amfana da tallafin kayan Sallah daga Shahararriyar Jarumar Masana’antar Kannywood Saratu Gidado wadda akafi sani da (Daso).
A wannan rana ne dai Saratu Gidado ta tara iyayen marayu mata domin basu tallafin kayan sallah Atamfofi kowacce turmi 1 domin sanya farin ciki a zukatan su da kuma zamar dasu tamkar Mazajen su ko iyayen su suna Raye.
Wasu daga cikin mata iyayen Marayun da suka amfana da tallafin kayan Sallah daga wajen Daso, sun Nuna Farin cikin su da kuma yin Godiya ga Saratu Gidado wadda ta taimaka musu da kayan sallah, musamman ta inda suka ce sun jima basu samu wanda yayi musu abin Alkhairin da Daso tayi Musu ba.

A nata bangaren Saratu Gidado wadda akafi sani da (Daso) ta Bayyana Dalilin da yasa tayi wannan Gagarumin aikin Alkhairin, inda tace tayi wannan rabon ne da Kudin Kamfanin ta na Daso Entertainment, wannan karon bata samu tallafi daga Hannun jama’a ba, kawai dai tayi amfani da Kudin da take samu a kamfanin ta ne.
A karshe tayi kira ga masu rike da Madafun Iko da masu hannu da shuni dasu dinga taimakawa marasa karfi ta bangaren kayan Abinci da kayan sakawa domin sanya farin ciki a zukatan su.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ