Jami’ar Chicago Ta Kulle Asusun X Biyo Bayan Ƙara Matsa Lamba Kan Bayanan Karatun Tinubu

Binciken ya kasa tantance dalilin da yasa cibiyar ta zabi iya wasu mutane ne kawai ke da damar shiga, sabanin yadda a baya kowa na iya lekawa domin duba abinda suke da bukata.

Alfijir Labarai ta rawaito Jami’ar Chicago ta kulle Asusunta na X wato Twitter daga sauran jama’a, yayin da ‘yan Najeriya ke kara matsa lamba kan takardar shaidar karatun shugaba Bola Tinubu mai cike da cece-kuce daga jami’ar.

Tare da alamar makullin da ke jikin asusun, binciken da Peoples Gazette ta yi a ranar Litinin ya nuna cewa “wasu Zaɓaɓɓun mabiyan” na cibiyar ne kawai za su iya ganin tweets yanzu, sabanin yadda yake a da.

Binciken ya kasa tantance dalilin da yasa cibiyar ta zabi iya wasu mutane ne kawai ke da damar shiga, sabanin yadda a baya kowa na iya lekawa domin duba abinda suke da bukata.

Har yanzu Jami’ar Jihar Chicago ba ta amsa bukatar Gazette na neman tsokaci kan bayanan ba, hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta cece-ku-ce a tsakanin ‘yan Najeriya masu rajin intanet kan bayanan karatun Mista Tinubu, inda da yawa suka yi kira ga jama’ar a kan X.

A farkon watan Agusta, Atiku Abubakar ya bukaci kotu ta amince da bukatar binciken karatun shugaba Tinubu.

Bayanan Tinubu sun kasance tare da CSU saboda ya yi imanin cewa takardun za su fayyace rashin daidaito a bayanan shugaban ciki har da takardun da aka samu a cikin 1970s mai dauke da sunan wata daliba Bola Tinubu wanda aka haifa a ranar 29 ga Maris, 1954.

Matakin da Abubakar ya dauka na shari’a, wanda ka iya fallasa tarihin karatunsa.

Tinubu ya kuma gabatar da bukatar hana wata kotun tarayya a Amurka sakin bayanan karatunsa ga babban abokin hamayyarsa a zaben shugaban kasa na 2023.

Cibiyar ta yi ikirarin cewa wani magatakarda ne ke da alhakin rashin bin ka’ida, wanda ya nuna takardar shaidar da makarantar ta sake buga da sunan Mista Tinubu, kamar yadda bayanan kotu da wakilinmu ya gani.

A yayin da ake ta cece-kuce a kan shari’a a Amurka, Mista Abubakar a ranar Lahadi ya yi wa Tinubu ba’a, inda ya nemi ya bayyana yadda ya samu digiri a Jami’ar Chicago ba tare da ya halarci makarantar firamare da sakandare ba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *