Jami’an Tsaron jamhuriyar Nijar Sun Cafke Mawaƙi Mista 442 Ola Of Kano

Alfijr ta rawaito Jami’an tsaron Jamhuriyar Nijar sun damke Mawaki Mr 442 da Ola, har an Aike dasu gidan Kaso

Fitaccen mawakin Hipop dinnan wanda aka fi sani da Mr_442 tare da abokin aikin sa Ola Of Kano, sun hadu da fushin hukuma a jamhuriyar Nijer bayan da suka aikata laifi mai girma.

Ɗaya daga cikin makusantan mawakin Murja Ibrahim Kunya ce, ta bayyana haka a shafin ta na TikTok.

Murja ta bayyana cewa tuni an aike da Mr 442 da abokin aikin shi zuwa gidan gyaran hali a Jamhuriyar Nijar tare da tarar aƙalla naira milyan goma kowannen su.

Murja ta bayyana irin laifin da suka yi inda tace, tunda farko mawakan sun yi yunkurin yin fasfo ne a Jamhuriyar Nijar, lamarin da ya zama babban laifi ga duk wanda ba dan kasar ba.

Mawakan biyu sun yi yunkurin yin fasfo din ne da niyyar samun damar haurawa kasashe da dama, duk da sun san cewa hakan babban laifi ne, inda suka yi aski da niyyar gujewa lamarin don kada a gane su yayin, yin fasfo din, sai dai kasancewar su fitattu hakan ya sa aka gane su tare da kama su.

Bayan da aka gano su an kama mawakan tare da kaisu gidan yari, wata majiya ta bayyana mana cewa wannan abinda sukai laifi ne babba a Nijar wanda zai iya sawa ayi musu hukuncin shekaru 6 kowanne a gidan yari.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *