Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’a ta Najeriya (JAMB), tare da umarnin Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, ta sanar da dakatar da karɓar sabbin ɗalibai a shirye-shiryen digiri da Kwalejojin Ilimi (Colleges of Education) ke gudanarwa tare da jami’o’i a matsayin haɗin gwiwa.
Rahotonni sunce wannan sabon tsari zai fara aiki daga zangon karatu na shekarar 2026/2027.
Sai dai ɗaliban da tuni aka riga aka ɗauka a waɗannan shirye-shiryen ba za su fuskanci wata matsala ba, domin za a ba su damar kammala karatunsu tare da samun takardun digiri kamar yadda aka tsara.
A maimakon tsarin haɗin gwiwa da jami’o’i, gwamnati ta ƙarfafa Kwalejojin Ilimi da suka cika ƙa’idoji su fara bayar da digiri kai tsaye ƙarƙashin sabon tsarin Dual Mandate, wanda ke ba su damar gudanar da shirye-shiryen NCE da digiri a lokaci guda ba tare da dogaro da jami’a ba.
Saboda haka, daga yanzu sabbin ɗaliban da ke neman shiga Kwalejojin Ilimi za su fi samun guraben karatun NCE, yayin da kwalejojin da suka samu amincewa za su iya gudanar da shirye-shiryen digiri da kansu.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t