Wata Babbar Kotu a Kano ta sanya 17 ga watan Afrilun 2024, a matsayin ranar da za ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje.
Alfijir labarai ta rawaito waɗanda ake tuhumar za a gurfanar da su a gaban kotu bisa tuhume-tuhume takwas da suka haɗa da zargin karɓar cin hanci, karkatar da kuɗaɗe da kuma almubazzaranci da dukiyar al’umma da kadarorin gwamnati.
A cikin takardar sammacin, sauran waɗanda ake ƙarar sun haɗa da Abdullahi Umar Ganduje, Hafsat Umar, Abubakar Bawuro, Umar Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad, Lamash Properties Ltd, Safari Textiles Ltd da kuma Lesage General Enterprises.
A ƙarar da Gwamnatin Kano ta shigar a kan waɗanda ake zargi su takwas, ta ce ta haɗa shaidu 15 da za su bayyana a gaban kotu.
An tsayar da ranar 17 ga Afrilun domin fara sauraron shari’ar wadda mai shari’a Usman Na’abba na babbar kotun jiha mai lamba huɗu zai jagoranta.
Babban Lauyan Gwamnati kuma Kwamishinan Shari’a na Kano, Haruna Isah Dederi, ya tabbatar da cewa Ganduje, matarsa da wasu mutane shida a ranar da aka bayyana.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk