Jam’iyyun adawa sun nuna damuwarsu game da batun zarge-zargen shugaban ‘yan sandan Imo.
Alfijir Labarai ta rawaito Shugaban yan sandan Najeriya Kayode Egbetokun ya magantu a gidan Talabijin na Channel akan harkokin tsaro a Abuja ranar 5 ga Nuwamba, 2023.
Hakan yqzo ne Kwanaki 11 ga Nuwamba, 2023 za a gudanar da zaben gwamna a jihohin Imo, Bayelsa da Kogi, babban sufeton ‘yan sanda na kasa (IGP), Kayode Egbetokun, ya bayyana sabon kwamishinan ‘yan sanda a jihar Imo, Mohammed Barde.
“Ina sane da cewa an yi ta yada zarge-zarge a shafukan sada zumunta kan kwamishinan ‘yan sanda a jihar Imo, amma saboda wannan zaben, muna canza kwamishinan ‘yan sanda a Imo,” in ji IGP
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar a ranar Lahadin da ya sanar a zauren gidan Talabijin na Channel.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp
