Iftila’i! Farashin Buhun Masara Ya Cike N100,000 A Wasu Kasuwanni Dake Nijeriya Da Sauran Farashin Kayayyaki Abinci

IMG 20240622 WA0191

Daga Aminu Bala Madobi

Bayan zagayen kuturunka nawa a wasu kasuwanni dake sassan Najeriya da wakilin Alfijir labarai yayi, kididdigar ta nuna cewa buhun masara yayi tashin gwouron zabi a kasuwar kasa-da-kasa ta Mile 12 dake Lagos.

A makon nan ana sayar da kowanne buhu mai cin kwano 40 a kan kudi ₦100,000, a yayin da a makon jiya aka sai da ₦87,000, a mako guda an samu karin ₦13,000 a jihar da ke kudancin Najeriya.

Ita ma dai kasuwar Mai’adua dake jihar Katsina, arewacin Najeriya buhun masarar ya kusa cika ₦100,000, inda aka sayar da buhunta kan kudi ₦95,000 a satin nan da ke mana ban kwana, bayan da a makon da ya gabata aka saya ₦84,000, karin ₦11,000 kenan aka samu.

A jihar kano a kasuwar Dawanau ₦85,000 aka sayi buhun masarar a makon nan, inda a makon da ya gabata aka saya ₦82,000, ita ma dai karin dubu 3 kenan aka samu a satin nan.

A kasuwannin jihohin Adamawa da Kaduna an sai da Buhunta ₦87,000 a wannan makon, amma farashin na makon jiya ya sha banban a kasuwannin, inda aka sayi buhun masara ₦85,000 a kasuwar Giwa jihar Kaduna a satin da ya shude, sai kuma kasuwar Karamar Hukumar Gombi a jihar Adamawa da aka saya ₦79-80,000.

Shinkafar Hausa kuwa ta fi sauki a kasuwar Mai’adua jihar Katsina da aka saya ₦145,000 a satin nan, amma a makon jiya ₦150,000 aka sayi buhunta, an samu ragin ₦5000 kan farashin makon da ya wuce.

Su kuwa Jihohin Adamawa da Kano da jihar Kaduna da ma Lagos, kuɗin buhun Shinkafa ‘yar gida ₦150,000 cif ne a wannan makon, hakan kuwa batun yake a makon da ya shude.

Ita kuwa Shinkafar waje ta fi tsada a kasuwar Giwa jihar Kaduna da ke arewacin kasar da ake siyarwa a ₦86,000, bayan da a makon da ya gabata aka saya ₦80,000

Sai dai farashin Shinkafar wajen bai sauya zane ba da na makon jiya wanda aka saya ₦85,000 a kasuwar Dawanau jihar Kano.

An sayi buhun Shinkafar waje ₦78-80,000 daidai a kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa a satin nan da ke dab da ƙarewa, inda a makon jiya aka sai da kan kuɗi ₦75,000.

A Mai’adua jihar Katsina ₦81,000 ne kuɗin buhun Shinkafar waje a satin nan, bayan a satin da ya gabata aka sayar ₦78,000.

Bari mu kammala Farashin Shinkafar waje da kasuwar Mile 12 International Market Lagos, da aka saya ₦83,000.

Kwalin taliyar Spaghetti ma dai ya fi tsada a kasuwar Mile 12 International Market Lagos da aka saya ₦17,000 a satin nan, yayin da a makon jiya aka sai da ₦16,000 karin ₦2000 a mako guda.

Sai kasuwar Mai’adua jihar Katsina da aka saya ₦15,000 a makon nan, bayan da a makon jiya aka saya ₦15,500
An samu ragin ₦500 kenan a makon nan.

A kasuwar Dawanau jihar Kano ₦13,500 ake sayar da kwalin taliyar a wannan makon, haka farashin yake a makon jiya.

Sai kasuwar Zamani da ke nan jihar Adamawa da aka sayi kwalin ₦14,000,inda a makon jiya aka saya ₦13,000 daidai.

To a kasuwar Giwa jihar Kaduna ma dai farashin bai sauya dana makon daya gabata da ake saidawa ₦14,000 cif.

Ga ma’abota cin kosai da alala kuwa Farashin farin wake ₦220,000 ne a kasuwar Mile 12 da ke jihar Legas a wannan satin,amma satin daya gabata ₦200,000 daidai a kasuwar.

Sai dai a kasuwannin jihohin Kano da Kaduna kuwa ₦175,000 aka sayar da buhunta a makon nan, yayinda a makon jiya aka sai da buhun kan kuɗi ₦170,000 cif.

₦160-170,000 ake sayar da buhun farin wake a kasuwar Gombi da ke jihar Adamawa a sati na, yayin da a satin da ya kare aka saya ₦160,000 daidai.

Da muka leka kasuwar Mai’adua jihar Katsina ma mun taras cewa ana sayar da buhun waken N170,000 a satin Nan, yayin da makon da ya gabata aka saya N165,000.

Saidai farashin ka iya hawa da sauka laakari motsi da tasarrafin yanayin kasuwa

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *