Yan daba sun kashe wani jami’in dan sanda yayin da wani fada tsakanin kungiyoyin ’yan daba guda biyu a unguwar Yakasai da ke birnin Kano.
Alfijir Labarai ta rawaito lamarin ya faru ne wajen misalin karfe 6:00 na yammacin Talata, lokacin da wani ɗan daba da ya sauka daga babur din Adaidaita Sahu a kusa da Asibitin kwararru na Maurtala Muhammad da ke Kano, abokan fada kuma suka hau shi da sara da suka.
Wani ganau ya bayyana cewar bayan saukar mutumin ne daga kan babur din sai wasu ’yan dabar da ba sa ga maciji suka far masa da makamai.
“Sai da ’yan sanda suka kwashe kusan minti 10 kafin su tarwatsa su, daga bisani ƴan dabar suka juyo kan ƴan sanda suka fara jifan su.
“Lokacin da ƴan sandan ke kokarin guduwa ne sai daya daga cikinsu ya fado daga kan mota, inda nan take ’yan dabar suka hau saran shi, ba ji ba gani, nan take ya ji gamu gidan gaskiya.
Majiyar ta kara da cewa an shafe tsawon kwanaki ana fuskantar fadan daba a unguwar, wanda mazauna unguwar ke cikin zulumi da rashin tabbas.
Wakilin daily trust ya tambayi Kakakin rundunar ƴan Sandan Jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce har yanzu ba su samu rahoton kisan ba, amma suna nan suna bincike a kai don gano gaskiyar abin da ya faru.
inda Ranka
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ
Allah Ya Kiyaye faruwar hakan nan gaba Ameen.
Allah ya qara kare mana ku