Ibtila’i! Wata Mummunar gobara ta tashi a ginin ‘yan sanda

FB IMG 1668071567049

An tura injinan kashe gobara wurin da lamarin ya faru, sai dai da alama suna fuskantar kalubale wajen kashe gobarar

Wata mummunar gobara ta tashi a wani ginin ‘yan sanda da ke Ismailia na gabar Mashigin Suez da ke Masar ranar Litinin, a cewar ganau da kafafen watsa labarai na kasar.

Wasu bidiyoyi da aka rika wallafawa a soshiyal midiya sun nuna yadda hayaki mai kauri yake tashi a ma’aikatar tsaro ta birnin, kuma da alama babbar kofar shiga ma’aikatar ta fadi.

Ganau guda biyu sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa an tura injinan kashe gobara wurin da lamarin ya faru, sai dai da alama suna fuskantar kalubale wajen kashe gobarar.

Kawo yanzu ba a sani ba ko gobarar ta yi sanadin mutuwa ko jikkatar mutane.

Majiyoyi a hukumomin tsaro na farin-kaya sun ce wasu bangarori na ginin sun fadi sakamakon gobarar.

Reuters

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *