Wani kwale-kwale dauke da dalibai ya kife a kogin Calabar-Oron a jihar Cross River da ke kudu maso kudancin kasar.
Alfijir Labarai ta rawaito Gidan talbijin Kasar NTA, ya bayyana cewa kwale-kwalen yana dauke da daliban da ke karatun aikin likita 14 yayin da ya kife.
A sakon da NTA ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Asabar da tsakar dare ya ce daliban, karkashin kungiyarsu ta NIMSA , sun je Calabar ne a wani bangare na bikin da suke yin shekara-shekara amma sai suka yanke shawarar shiga kwale-kwale don kashe kwarkwatar idanunsu a wurin shakatawa na Calabar Marina.
Sai dai “abin takaici shi ne kwale-kwalen ya kife” amma dalibai 14 sun yi sa’a bayan da jirgin rundunar sojin ruwa na kasar, wanda ke kusa da su a lokacin, ya yi gaggawar ceto su.
Amma har yanzu ba a ga dalibai uku ba kuma ana ci gaba da nemansu, a cewar NTA.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ