Ibtila’i! Helikwaftan Rundunar Sojin Nijeriya Ya Yi Hatsari

Helikwaftan yana kan hanyarsa ta tafiya Kaduna ne bayan da ya bar Makarantar Firamare ta Zungeru. Hoto: Nigerian Airforce

Alfijir Labarai ta rawaito Wani jirgi mai saukar ungulu na rundunar sojin saman Nijeriya ya yi hatsari a kusa da kauyen Chukuba da ke Jihar Neja a yankin tsakiyar kasar.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe daya na rana agogon Nijeriya a ranar Litinin, kamar yadda sanarwar da rundunar sojin saman ta fitar mai dauke da sa hannun daraktan watsa labaranta, Air Commodore Edward Gabkwet, ta bayyana.

“Helikwaftan yana kan hanyarsa ta tafiya Kaduna ne bayan da ya bar Makarantar Firamare ta Zungeru inda daga baya aka gano ya fadi a kauyen Chukuba da ke karkashin karamar hukumar Shiroro,” kamar yadda sanarwar ta ce.

Rundunar ba ta bayar da rahoton ko an rasa rayuka a hatsarin ba, amma ta ce ana aikin ceto matukan jirgin da fasinjojin da ke cikinsa, sannan an kaddamar da binciken farko don gano musabbabin hatsarin.

TRT Afrika

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

One Reply to “Ibtila’i! Helikwaftan Rundunar Sojin Nijeriya Ya Yi Hatsari”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *