Ibtila’i! Guguwar Iska Ta Lalata Gidaje Sama Da 450 A Kuletu Dake Karamar Hukumar Dass A Jihar Bauchi

FB IMG 1750100456996

A yammacin jiya Lahadi da ta gabata iskar guguwa mai karfin gaske ta lalata tare da ruguza gidaje sama da 450 a unguwar Kuletu dake ƙaramar hukumar Dass.

Guguwar ta fara ne da misalin karfe 4:47 na yamma inda ta ruguje tare da shafe gidaje 50 zuwa baraguzai da yaye rufin kwanon sauran gidajen da abin ya shafa, wani mazaunin garin Jibrin Abdullahi da yanzu yake jagorantar aikin tantance ta’adi da barnar da iskar tayi ya shaida ma wakilinmu cewar, yanzu haka sunyi kiyasin gidaje 452 da iskar ta lalata kuma suna cigaba da aikin tantancewar. Ya nemi dauki daga hukumomin gwamnati da abin ya shafa kamar SEMA, NEMA da gwamnatin jihar Bauchi domin rage wahalhalu ga wadanda abin ya shafa musamman wurin kwana da abinci.

Jibrin Abdullahi, yace tunda suke ba su taba ganin bala’i mai tada hankali irin wannan ba ganin yadda iskar tayi karfi kamar zata tada garin, ya roki jama’a da su taimaka musu da addu’oi domin samun sauki.

Ga Masu Son Bada Talla A Kira   +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zN

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *