Ibtila’i! Gobara Ta Lalata Tarin Dukiya A Wani Dakin Ajiyar Kaya

Gobara ta kone wani dakin ajiyar kaya a wani bene mai hawa uku da ke lamba 64 Venn Road a Onitsha.

Alfijir Labarai ta rawaito wata Gobara a ranar Talata ta kone wani dakin ajiyar kaya a wani bene mai hawa uku da ke lamba 64 Venn Road a Onitsha, Anambra.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban hukumar kashe gobara ta Anambra, Martin Agbili, a ranar Laraba.

Mista Agbili ya ce hukumar kashe gobara ta samu kiran tashin gobara a wani bene mai hawa uku da misalin karfe 9:46 na dare. ranar Talata.

“Nan da nan muka tura motocin kashe gobara da jami’an kashe gobara zuwa inda gobarar ta tashi.

Ba a san musabbabin tashin gobarar ba kuma ba a rasa rai ba,” Mista Agbili ya bayyana.

“Gobarar ta shafi ginin kuma ta shafi kayan da ke benen, saboda dumbin kwalabe da ke cikin ma’ajiyar sun lalace.”

Mista Agbili ya kara da cewa jami’an kashe gobara sun sami nasarar shawo kan gobarar daga yaduwa zuwa wasu gine-ginen da ke kewaye.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/BW0j8s7exuQ7ojpyCVMtfI

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *