Ibtila’i! Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje Sama Da 200 A Jihar Sokoto.

B9

Daga Aminu Bala Madobi

Bayan zuwan damuna, da yawa daga cikin mazauna karamar hukumar Gada da ke jihar Sokoto sun rasa matsuguni, gonakinsu, da gidaje kusan 228 da dabbobinsu sakamakon ruwan sama da aka yi a kwanakinnan nan.

Binciken da Alfijir labarai tayi ta gano cewar daga cikin al’ummomin da lamarin ya shafa sun hada da Dantudu, Balakozo, Gidan Tudu, da kuma garin Tsitse.

Sakamakon tantancewar da hukumar bada agajin gaggawa ta kasa (NEMA) da hukumar bada agajin gaggawa ta Jihar Sakkwato (SEMA) suka gudanar a yankin, da lamarin ya fi shafa shi ne kauyen Dan Tudu, inda gidaje 62 da gidaje 71 suka shafe a kauyen Balakozo kuma gidaje 33 da gidaje 48 ne lamarin ya shafa.

Hakazalika lamarin ya shafi gidaje 38 da gidaje 52 a kauyen Gidan Tudu, gidaje 68, da kuma 89 a cikin garin Tsitse duk a karamar hukumar ta Gada.

Adadin mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Dan Tudu, Balakozo, Gidan Tudu, da garin Tsitse sun kai 1,664.

Hukumomin sun tabbatar da cewa dabbobi da dama da suka hada da tumaki da awaki sun bace saboda rugujewar gine-gine a lokacin ruwan sama.

Allah ya kara karewa ameen.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *