ibtila I! wata Ma adanar Mai Ta Kama Da Wuta An Samu Asarar Rai Da Dukiya Da Gidaje A Kano

IMG 20240109 WA0212

Wata fashewa daga wata ma adanar mai da ake zargin ba bisa ka’ida ba a Kano a ranar Litinin, 8 ga watan Janairu, ya kashe mutum daya, ya kone akalla gidaje biyar da wata babbar mota.

Alfijir labarai ta rawaito Lamarin ya faru ne a unguwar Katango General dake Wailari, ta hanyar Western Bypass, daura da gidan Maryam Shekarau, dake kan titin Ring, Kano.

Kimanin sa’o’i uku aka kwashe tare da hadin gwiwar jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Kano da hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA da ma’aikatan kashe gobara daga gidan man Salbas wajen shawo kan gobarar.

Wani direban babbar motar da ake kira Aminu da ke cikin matatar man, ya kone kurmus ba a iya gane shi.

Jami’an hukumar kashe gobara sun gano gawar sa, yayin suka isa wurin da lamarin ya faru bayan isarsu Wajen.

“Gidaje biyar sun kona da kurmus sakamakon gobarar da ta girgiza mazauna unguwar,” in ji wani ganau.

An ceto wata tsohuwa da ta kasa tafiya daga daya daga cikin gidajen. Haka kuma, an ceto wasu yara biyu daga wani gida, wanda mahaifiyarsu ta fita a guje ta bar su a ciki.

Ahmad Umar Gaya, ma’aikacin ofishin duba ababen hawa (VIO), ya shaida wa manema labarai cewa, yana bakin hanya ne ya ji karar fashewar wani abu.

“Wurin, wanda ke tsakiyar gidajen zama a Katango a Wailari, ana amfani da shi ne wajen adana tarkacen manyan motoci da tireloli da kuma tace man injin da aka yi amfani da shi don wasu dalilai.

“Babu wanda zai iya bayyana ainihin abin da ya faru wanda ya kai ga fashewar. Tirelar da ke dauke da ganguna na man inji da ake yi amfani da su ta kone sakamakon gobarar, shima direban ya kone kurmus.

“A kusa da wurin akwai gidaje da mata da yara, kuma kusan gidaje biyar ne gobara ta kone.”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *