Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da afkuwar gobarar da ta tashi a safiyar Larabar da ta gabata da ta kone ofisoshi 17 a sakatariyar karamar hukumar Gwale.
Alfijir labarai ta rawaito Jamiโin hulda da jamaโa na hukumar Alhaji Saminu Abdullahi ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a Kano.
Abdullahi ya ce lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Laraba.
โMun samu kiran waya da misalin karfe 03:43 na safe daga Abdullahi Hassan cewa gobara ta tashi a sakatariyar Gwale.
โBayan samun labarin, mun aika da motar kashe gobara zuwa wurin da abin ya faru da misalin karfe 03:46 na safe domin shawo kan gobarar,โ inji shi.
Abdullahi ya ce benen da aka yi amfani da shi a matsayin ofis mai tsawon kafa 300 x 200 da sauransu, wanda ya kai 17, ya lalace gaba daya.
Ya kuma ce an kona motar motar kirar Peugeot 406, motar Haice guda daya da motar daukar marasa lafiya ta tasha.
Ya ce hukumar na binciken musabbabin tashin gobarar.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai ๐๐
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp