Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta gayyaci tsohon Gwamnan jihar Abdullahi Ganduje bisa bidiyon Dala.
Alfijir Labarai ta rawaito idan zaku iya tunawa a shekarar 2017 dai ne jaridar Daily Nigerian ta wallafa wasu hotunan bidiyo, in da ake zargin tsohon da karbar wani abu mai kama da cin hanci daga hannun ‘yan kwangila.
Sai dai tsohon Gwamnan ya musanta wannan zargi, in da yace bidiyon ba shi da sahihanci, ma ana dai kalan sharri ne kawai.
Barr Muhyi Magaji Rimin-Gado shugaban hukumar yaki da rashawa ta jihar a ranar Laraba ya ce binciken kwakwaf ya tabbatar da sahihancin bidiyon.
Sai dai a ranar Alhamis, Barr Rimin-Gado ya ce hukumar ta gayyaci tsohon gwamnan domin ya amsa tambayoyi daga hukumar, biyo bincike da hukumar ta ce ta gayyato masu binciken kwakwaf sun kuma gudanar da ayyukansu.


Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ