Hukumar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta ce ta fara binciken batan kudaden gwamnati sama da Naira biliyan 4 daga kamfanin samar da noma na jihar Kano, KASCO.
Alfijir Labarai ta rawaito shugaban hukumar Muhuyi Rimin gado ne ya tabbatar da haka a lokacin da ya jagoranci wani rangadin bincike a rumfunan da aka ajiye motoci da manyan taraktoci da ake kyautata zaton an sayo su ne da kudaden da aka bankado a karamar hukumar Kumbotso ta jihar.
Rimin Gado ya ce an karkatar da kudaden ne daga KASCO zuwa wata kungiya mai rijista da Hukumar Kula da Kamfanoni, mai suna Association of Compassionate Friends.
“An samar da kungiyar ne don inganta tare da kula da rayuwar ‘ya’yan marasa galihu a cikin al’umma, amma abin takaici sai aka mayar da ita wata na’ura mai satar dukiyar jama’a,” in ji shi.
Shugaban ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kano ana ciro wadannan kudade ne a matsayin tallafi ga hukumar KASCO, amma an zaftare su ne ta hanyar amfani da kungiyar masu rijista da wani kamfani na farautar dutse.
“Mun kama mutane takwas da ake zargi da bayyana sahihan bayanai ga hukumar.
“Daya daga cikin su ya ce an ba shi wasu kudi ne don ya yi karya a KASCO, amma ya ajiye kudin a gefe yana jiran wani lokaci kamar haka, kuma da radin kansa ya mayar da kudin.
“Ya zuwa yanzu, mun kwato Naira miliyan 15 kuma mun yi nasarar dakile kusan Naira miliyan 8,” in ji shi.
Rimin Gado ya ce hukumar na da shakkun yadda ake yin wasu hada-hadar kasuwanci tsakanin kamfanonin da wasu bankuna, yana mai jaddada cewa za a iya gayyatar wasu manajojin bankin domin warware wasu batutuwa.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb