Alfijr ta rawaito hukumar Kula da harkokin man fetur ta kasa NMDPRA da ke Kano, ta rufe gidajen mai 14, bayan da ta kiskesu suna sayar da man a kan farashin da ya wuce kima.
Da yake yi wa manema labarai karin haske game da sintirin da suka yi ranar Alhamis, Jami’in hukumar a Kano, Aliyu Muhammad Sama, ya ce duk da dai a yanzu babu tsayayyen farashin fetur din a hukumance, amma gidajen man kan sayar da shi a farashin da ya wuce hankali.
Ya Kara da cewar rufe gidajen man ya zama wajibi bayan da aka gano suna sayar da fetur tsakanin N290 zuwa N300 kan kowace lita.
Idan zaku iya tunawa, a watan Disamban bara, hukumar ta rufe gidajen mai sama da 100 na ‘yan kasuwa saboda sayar da shi sama da farashin da ya kamata. In Ji shi.
Sama ya ce hukuncin wadanda lamarin ya shafa shi ne tarar N150,000 kan kowane famfo, sannan gidan man zai ci gaba da zama a rufe zuwa lokacin da ya amince ya sayar da fetur din a kan farashin da ya dace.
Hakazalika ba mu kai ga gurfanar da ‘yan kasuwar da lamarin ya shafa a gaban kotu ba saboda hakan shi ne matakin karshe.
“Za mu ci gaba da farautar gidajen man da ke sayar da fetur din a kan farashin da ya wuce kima,” in ji shi
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇