Hukumar Kiyaye Hadurra Ta Kasa Ta Kori Jami’inta Kan Shiga Zanga-Zangar NLC

Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), reshen jihar Imo, ta kori daya daga cikin jami’anta saboda halartar zanga-zangar da ta gudana a ranar Laraba karkashin jagorancin kungiyar kwadago a cikin wata riga ta musamman.

Alfijir Labarai ta rawaito Kwamandan hukumar ta FRSC a Imo, Evaristus Ebeniro, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da fitar.

Ya bayyana cewa an cire jami’in ne daga mukaminsa kuma ba jami’in hukumar ba ne yanzu haka.

Idan zaku iya tuna cewa kungiyoyin kwadagon Najeriya NLC da TUC sun gudanar da zanga-zanga a fadin kasar domin nuna rashin jin dadinsu da cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi.

Ebeniro ya ce duk da cewa mai zanga-zangar babban jami’i ne na musamman, amma tun daga lokacin an cire shi, kuma ba ya rike da katin shaida na musamman.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/BW0j8s7exuQ7ojpyCVMtfI

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *