Hukumar Kidaya Ta Sanar Da Ranar Fara Kidayar Jama’a


Alfijr ta rawaito Hukumar kidayar jama’a ta Kasa ta sanar da ranar 3 ga watan mayu a matsayin ranar fara kidayar jama’a da gidaje ta 2023, kamar yadda gwamnatin tarayyar Najeriya ta tabbatar.

Wani mamba a kwamitin yada labarai da wayar da kan jama’a kan kidayar jama’a da gidaje ta kasa a shekarar 2023, Dr Garba Abari, ya tabbatar da hakan a Abuja ranar Lahadi a lokacin da ya bayyana a matsayin bako a dandalin kamfanin dillancin labarai na Kasa NAN.

Abari ya bayyana cewa, za a fara atisayen na kwanaki uku ne a ranar 3 ga watan Mayu, kuma za a kammala a ranar 5 ga watan Mayu a fadin jihohi 36 na Nijeriya, ciki har da babban birnin tarayya (FCT).

Ya ce, “Wannan canjin da INEC ta yi ya sa ya zama wajibi mu ma mu daidaita ranar da za a gudanar da aikin.

“Dole ne a gabatar da kidayar daga ranar farko ta 29 ga watan Maris zuwa 2 ga watan Afrilu,wanda ya zuwa yanzu aka sauya ranar zuwa 3 da 5 ga watan Mayu.”

Idan za’a iya tunawa KakakiHausa ta rawaito cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta gudanar da kidayar jama’a a shekarar 2006.

 
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

2 Replies to “Hukumar Kidaya Ta Sanar Da Ranar Fara Kidayar Jama’a

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *