Hukumar Hisbah Ta Fitar Da Kaidoji Ga Masu Gidajen Wasanni Da Za Su Kiyaye A Lokutan Bukukuwan Sallah A Kano
1 Ba’a Yarda Da Shigar Da Kananan Yara Gidajen Wasanni Ba.
2 Ba’a Yarda Da Chakuduwar Maza Da Mata Ba.
3 Duk Lokacin Sallah Za’a Dakatar Da Wasa Domin Yin Sallah.
4 Ba’a Yarda Da Shiga Da Duk Wani Nau’in Makamiba.
5 Ba’a Yarda Da Sayarda Kayan Maye Kosha a Gidan Wasa Ba.
6 Ba’a Yarda Da Shigar Banza Ba Daga Bangaran Maza Ko Mata.
7 Ba’a Yarda a Bawa Yan Daudu Damar Gabatar Da Ko Wane Irin Wasa Ba.
8 Dolane a Kaucewa Sanya Wakokin Batsa Ko Makamancin Haka.
9 Ba’a Yarda Da Rawar Mace Da Namijiba.
10 Dole Duk Gidan Wasa Su Tashi Kafin Lokacin Salar Magariba.