Alfijr ta rawaito Jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) sun gano wasu makudan kudade na biliyoyin Naira da aka jibge a gidajen wasu gwamnonin da ke kan karagar mulki.
Wasu majiyoyi a ranar Juma’a sun bayyana gwamnonin kamar haka, Nyesom Wike na jihar Ribas, Bello Matawalle na jihar Zamfara da Abdullahi Ganduje na jihar Kano, a wata tattaunawa ta musamman da Sahara Reporters.
Shugaban Hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa a baya ya ce ana sa ido kan gwamnonin jihohi uku da ke kan karagar mulki a kan yunkurin da suka yi na karkatar da biliyoyin Naira ta hanyar biyan albashin ma’aikata.
Wannan ci gaban ya biyo bayan sanarwar da babban bankin Najeriya (CBN) ya bayar na cewa zai sake fasalin wasu takardun kudi na Naira.
Yayin da shugaban na EFCC ya ki bayyana sunayen gwamnonin uku, wasu majiyoyi da dama a hukumar yaki da cin hanci da rashawa sun bayyana sunayen gwamnonin, Wike, Ganduje da Matawalle na Ribas, Kano da Zamfara ga Sahara Reporters.
Wani babban jami’in EFCC ya shaidawa SaharaReporters cewa, “Gwamnoni uku da muke sa ido a kai su ne, Gwamna Wike, Matawalle da Ganduje na Kano, an gano biliyoyin Naira da aka jibge a gidajensu a Abuja, Fatakwal da Kano. “
An kama wadannan gwamnonin jihohi uku suna kokarin kwashe wadannan makudan kudade da aka ajiye a gidajensu bayan da babban bankin kasar CBN ya bayyana kudirinsa na sake fasalin kudin Naira.
“Suna da biliyoyin kudi; na Ganduje a Kano kawai yake ajiyewa amma ya yi amfani da wasu sassa wajen biyan kudin otel da ya gina a Abuja.
Otal din yana bayan cibiyar taron sojojin saman Najeriya.”
“Gwamnan Zamfara, Matawalle ya ajiye nasa a wasu gidajen da ya mallaka a Abuja yayin da Wike na da nasa a ajiye a Abuja da Fatakwal,” in ji daya daga cikin majiyoyin.
2018, Bidiyon Ganduje guda biyu da ake zargin ‘yan kwangilar yana karbar cin hanci da rashawa sun yadu a shafukan sada zumunta, faifan bidiyon da jaridar Daily Nigerian ta wallafa, sun nuna gwamnan yana karbar makudan kudade yana sanya su a cikin babbar rigarsa
An rahoto cewa gwamnan ya bukaci dala miliyan 5 daga hannun ‘yan kwangilar da suka nada faifan bidiyon a lokacin da suke mika masa wani bangare na kudin, a daya daga cikin faifan bidiyon gwamnan ya karbi dala 230,000, wanda ya ke cusawa a cikin Babbar Riga.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb
Shahara Reporters
Kaiyama Muhammad wannan hk akeso
Hahahaha