Hukumar EFCC Ta Kwato Naira Biliyan 60 A Cikin kwanaki 100 – In ji Olukoyede

FB IMG 1708967455645

Shugaban hukumar yaƙi da yi wa tattalin arzikin ƙasa ta’annati ta EFCC, a Najeriya, Mista Ola Olukoyede, ya ce a cikin kwana 100, ofishinsa ya samu ƙorafe-ƙorafe 5,000 da suka danganci almundahana, kuma ya samu ƙwato N60bn.

Alfijir labarai ta rawaito a cewar shugaban, hukumar ta samu ƙwato wasu $10m, a wannan tsawon lokacin, kamar yadda wasu jaridun ƙasar suka ambato.

Haka kuma a cewar shugaban EFCC, hukumar ta samu nasarar yankewa mutane 700 hukunci, kan batutuwan da suka shafi kuɗaɗen da aka ƙwato, a ƙasa da watanni huɗu.

Inda ya ƙara da cewa haɗa hannu wuri guda da al’umma na da muhimmanci, domin a cewarsa batun na da girma sosai ta yadda hukumarsa kaɗai ba za ta iya ba, sai al’umma sun taimaka wajen bayar da bayanai idan sun ga wani abu.

Mista Olukoyede ya bayyana cewa “idan har zan iya ƙwato naira biliyan 60 a ƙasa da kwana ɗari, me kake tunani game da yawan dukiyar da ake sacewa. “

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *