Rundunar ‘Yan Sandan jihar Jigawa hadin Gwiwa da hukumar tsaro ta DSS sun cafke wani likitan karya mai suna David Samuel dake sana’ar sayar da magani a birnin Dutse.
Alfijir Labarai ta rawaito wanda ake zargin dai yayi karyar cewa shi kwararan Likita ne wanda ke aiki a Asibitin Rashid Shakoni dake Dutse harma ya bude wani kantin sayar da magani mai suna Shawai Medical Plus dake Unguwar Mopol-Base a Dutse.
Bayan fara gudanar da bincike jami’an tsaro sun samu wanda ake zargin da takardar kammala karatun Degree na Jami’ar Danfodiyo dake Sokoto da takardar shaidar yiwa kasa hidima dana mamba a kungiyar likitoci ta kasa, inda daga karshe wanda ake zargin yace duk na Karya ne, hasalima shi korarran dalibi ne a Jami’ar ta Danfodiyo.
Jami’in hulda da jama’a na Rundar DSP Lawan Shisu Adam yace zasu gurfanar da wanda ake zargi a gaban kuliya manta sabo bayan kammala zizirfan bincike.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb