Babban daraktan hukumar Mallam Abba Sufi ne ya tabbatar wa da Yan Jaridu kamen.
Alfijir labarai ta ruwaito a wata hira da BBC, Sufi ya ce hukumar ta kama shi bayan jerin gargaɗin da ta yi masa sakamakon abubuwan da yake wallafawa a shafukan sada zumunta.
A cewar sa ”Mun kama shi ne bayan tarin gargaɗin da nasiha da muka sha yi masa kan abubuwan na baɗala da rashin kunya da yake wallafawa shafukansa na sada zumunta.”
Sufi ya ce hukumar Hisba za ta gurfanar da shi matashin a gaban kotu ranar Litinin
Al’amen G-Fresh dai ya yi fice a shafukan sada zumunta musamman TikTok, inda yake wallafa bidiyoyin da ba su dace ba, lamarin da ya sa hukumar Hisbar ta ce ta yi masa gargadi da nasiha amma bai ɗauka ba.
A baya dai G-Fresh ya auri Sadiya Haruna (itama ma’abociyar amfani da shafukan sada zumunta na Zamani), amma ba su jima ba, auren ya rabu lamarim da ya kai su har ga kotun Musulunci a jihar.
Anjima ana kai ruwa rana kan batun auren nasu, amma daga ƙarshe G-Fresh ya sauwaƙe wa Sadiya Haruna, bayan ta biyasa diyyar Naira 500,000.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj